input license here

Muhimmancin auren soyayya

Auren soyayya ya kasance aure mafi dadin zama ga ma'aurata. Muddin masoya guda biyu su ka auri junansu, fo za su yi zamantakewa ta soyayya a cikin gidansu ba tare da fuskantar wani kalubale ba.
Jituwa ne abu na farko da ke faruwa a tsakaninsu.
Ga wasu abubuwa da auren soyayya ke haifarwa ma'aurata kamar haka:
Samun yaya na gari
Samun rayuwar farin ciki
Samun ahali masu kyakkyawar fahimta
Dorewar zumunci tsakanin dangi na kusa da na nesa da dai sauransu.
Dalilin faruwar hakan kuwa shi ne irin yadda rayuwar masoya ke kasancewa ta musamman mai dauke da kula da juna, da fahimtar juna, da kare mutunci ko  mutunta juna, da dai sauransu.
Tabbas mutanen da su ka yi auren soyayya su ne wadanda za su ci moriyar zamantakewa mai kyau. 
Duk da dai rayuwa ta gaji zo mu zauna zo mu saba, amma muddin dai aka ce auren soyayya ce aka yi to komai zai zo cikin sauki. Abin nufi a nan shi ne, idan sabani ya zo a tsakani to tabbas za su fahinci junansu ne a cikin sauki ba tare da sun zurfafa wajen zargin juna ba.
Related Posts
SHARE

Related Posts

Subscribe to get free updates

Post a Comment