input license here

Sakon soyayya mai tsuma zuciyar masoya


Assalu a laikum, ya ke tumfafiya mai taken farin jini, fure mai janhankalin dukkan halittu mutum ko dabba, tsuntsaye ko aljan.
Hakiki rayuwa maras dandano ta tabbata ga dukkan ruhin da ke rayuwa ba tare da ke ba.
A yanzu na tabbatar da cewa, babu wani nau'in kayan dadi da zai iya gusar min da damuwata ba sai soyayyarki.
Ya ke abar kaunata, na fada cikin kogin soyayyarki ina neman nutsewa, ki taimaka ki tallafa ki agajewni ta hanyar tsamoni da sanyayan kalaman soyayya da ke fitowa daga daidaitaccen bakinki mai dauke da lallausan lebe da ke ruda masu sauraronki.
Related Posts
SHARE

Related Posts

Subscribe to get free updates

Post a Comment